作词 : Hamisu Breaker
作曲 : Hamisu Breaker
Beat amjad records
Ashe da rai nake sonki jaruma
ba da zuciyata ba
Komai ruwa da iska a kanki
ba za na daina kewa ba
Idan na samu zarar samunki
ba za na tanka kowa ba
Ni ban ga mai harara ba
ɓalle na waiwaya ah
In dai a kanki ne za na jure wahalar zuwa garin nisa
Da an taɓa ki a jira ni
Don kuwa tilas sai na zo na ɗau fansa
Jimirin jiranki na yi
Don ki zo na kalle ki gimbiyar Hausa
Sirri na rayuwata ke ce kawai da kin kira da na amsa
Zuma a baki daɗi gare ta
kin ba ni taki na lasa
In dai a kanki ne na yi nisa don ba kiran da zan amsa
Tilas ganinmu, tilas barinmu, ƙaunarki tun da na yi nisa
Sam ba batun na fasa ko za a ce mun in ba da rai fansa
Tsarin zubinki daidai ne
Ya kama zuciyata ne
Ina jin kamar mafarki ne
Ina sonki, so mataki ne
Ni ba ni da damuwa in har zan buɗe ’yan idanuna
Na kalle ki ga ki daf da ni
to me za ya damu ƙalbina
Yauwa za na yi amo tun da na gane kina da tausayina
Don yanzu na zamo ya mafatauci mai biɗar gurin kwana
Na ƙwalla shela don sanar da iya maƙiya kalamaina
Daga zuciya nake kwatanta ina zayyano jawabaina
Idan babu ke ina ne zan saka zuciyata bar yawan ƙuna
Kowa da nasa amma ni ke ce cikar muradaina
Yau ga ni a ruwa kusa da kada, zo ki ceci ƙarkona
Komai da mafita
kar da ki saba da furta ban kwana
Ina ji ina gani yadda nake sonki ya fi ƙarfina
Na san a duniya da wanda yake janye duk tunanina
Soyayya rayuwa wani sa’in sai ta zama wutar ƙuna
Duk wanda ke cikinta shi ne jurau amma fa a wurina
So na faranta rai da ruhi
ya sa ka zama kamar sarki
Kuma rayuwa da so misali ne na kama da a mafarki
Samari mu yi haƙuri idan har mun samu so mu sa sauƙi
’Yan mata mu yi haƙuri idan har mun samu so mu sa sauƙi
Masoyi yana da rana ne
Masoyi yana da rana ne
Masoyi yana da rana ne
(Midget mix)